Gobara ta canye shaguna 180 ƙurmumus a babbar kasuwar Sakkwato


Gobara ta canye shaguna 180 ƙurmumus a babbar kasuwar Sakkwato


Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar jihar Sokoto da safiyar yau Litinin ta yi sanadin ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna.


Garba Muhammad Gwazi, shugaban ƴan mashin reshen jihar ya shaida wa BBC cewa gobarar ta laƙume shaguna ‘180’ na masu sayar da mashin.

A cewarsa, har yanzu ba a san abin da ya janyo tashin gobarar ba da ta janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira. Sai dai ya ce gobarar ta soma ne daga wata shara da aka tara.

BBC ta ƙara da cewa, ya bayyana cewa gobarar ba ta kai ga asarar rai ko jikkata ba.

Gwazi ya kuma yi kira ga gwamnati ta kai masu ɗauki domin “kasuwancinmu ya miƙe ya ci gaba.” in ji shi.