Jamila Labarina itace uwar Haidar Adam a Zango Kuma itace matarsa ta farko a duniya


Jamila Labarina itace uwar Haidar Adam a Zango Kuma itace matarsa ta farko a duniya

Kamar yadda muka sani cewa jarumar nan taku ta Shirin nan naku Mai garin jini wato Shirin Labarina Wanda kamfanin Saira movie ke gabatarwa a tashar arewa24 da Kuma YouTube channel nasu Mai suna Saira movies ako Wanne ranar jumaa na karshen mako.


Wannan jarumar wasu na tambaya cewa shin tsohuwar matar jarumin nan ce Adam a Zango koya ne ?

Jamila dai yadda kuka Santa a wannan Shirin na Labarina itace matar jarumin nan Adam a Zango ta farko wadda ya fara aura Kuma itace uwar dansa Haidar Wanda shine yaronshi na farko a duniya.


Kamar yadda wasu ke ta tambaya Akan menene silar rabuwar su ta aure ?

Shidai mutuwar aure lokacine Kuma ance Mai daki shine kadai yasan inda dakinsa keyimasa yo-yo Don hakan wannan tambayar abakin jaruman biyu yakamata aji amsar ta.

Jamila ta kasance itace jaruma ta farko data fara auran jarumin nan naku wato Adam a Zango tun tana farkon Shiga a masana Antar ta kannywood kamar yadda kuka sani bata fi yin wasan Hausa 2 zuwa 3 ba sukayi aure ganin irin soyayya dake tsakaninsu da ita Kuma Allah yabasu arzikin samun da namiji.

Muna yi Mata fatan alheri akoda yaushe..