YAU Shekaru 22 Da Rasuwar Balaraba Muhammad - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

YAU Shekaru 22 Da Rasuwar Balaraba Muhammad

Mar 16, 2024


YAU Shekaru 22 Da Rasuwar Balaraba Muhammad


A yau Asabar, 16 ga watan Maris na shakerar 2024, tsohuwar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Balaraba Muhammad ta cika shekara 22 daidai da rasuwa a lissafin kalandar Girigoriya. 


Marigayiyar dai idan za a tuna, ta rasu ne a ranar Asabar, 16 ga watan Maris na shekarar 2002 a sakamakon mummunan hatsarin mota da su ka yi akan hanyar kawo ta ɗakin mijin ta daga Kaduna zuwa Kano bayan ɗaura auren ta da fitaccen jarumi Shu'aibu Lawal wato Kumurci. 


Marigayiya Balaraba, wacce yaya ce ga jaruma Maryam Muhammad (Malika) jaruma wadda ta yi farin jini a ɗabi'ar ta na girmamama jama'a. Ta kuma yi tashe sosai a lokacin da ta ke yin Fim kamin auren ta da Kumurci.


Wasu daga cikin fina-finan da ta fito a ciki lokacin rayuwar ta sun haɗa da Dawayya, Matar Uba, Zainab, Tasiri, Maryam, Burin Zuciya, Rigar Ƴanci, Tawakkali 2, Furuci, Dafa'i da sauran su da dama.


Da fatan Allah Ya ci gaba da kai haske kabarin ta da saura al'ummar musulmi gaba ɗaya. Amin.