-->
Ku tayani addu’a na samu mata ta har abada albarkacin daren Lailatul Qadir – Adam a zango

Ku tayani addu’a na samu mata ta har abada albarkacin daren Lailatul Qadir – Adam a zango


Ku tayani addu’a na samu mata ta har abada albarkacin daren Lailatul Qadir – Adam a zango


Fitaccen Jarumi a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya nemi al’ummar musulmai su taya shi da addu’a Allah Ya ba shi matar aure wacce ba za su taɓa rabuwa ba har abada.


Jarumi adam a zango ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta Instagram inda yake neman al’umma musulmi da su tai make shi da addu’a.“Dan Allah ku saka ni a addu’arku Allah Ya bayyana min matar da zan aura a cikin wannan wata mai albarka Daren Lailatul Qadir. Matar da zan yi alfahari da ita Duniya da Lahira. Allah Ya sa mutuwa ce kaɗai za ta raba ni da ita”


Adam a zango wanda yake ana rade-rade auri saki yake wanda a wata fira da bbchausa da ya taɓayi ya nuna rashin jin dadin sa da mutane suke jefa masa wannan kalma ta auri saki.


Hausaloaded ta tattaro martanin mutane a karkashin rubutun.


@ummabamalli tana cewa : Ubangiji Allah ya baka mata tagari wadda zaku fahimci juna kuma idan anyi yasa mutuwa zata raba.


@aamadaz yana cewa : In sha Allah zaka samu Ba Ado, Ina rokon Ubangiji ya baka mai addini da dabi’a.


@nafisatu_gayu tana cewa :


Allah Ya Amsa Maka, sannan Don Allah idan zaka Nemi matar aure Ku dena biyewa kyau ko Fari ko duniya, Mafi yawan irin wadan Nan Matan wllh basa zaman Aure Musamman ma kyawawa suna amfani dakune kawai wajen Dauka Ka kansu daga Nan su kujeku Su fita yawan Duniya Suma sun zama cele kenan , wllh Mafi yawan matan da kuke aure Dauka Kar ku Kawai Suke Aure Baku ba, Allah Ya Hadaka da mace ta gari Alfarmar Shugaba S A W .


@maman_ilham_agadaz tana cewa :


Kaima kazama na kwarai sannan kanemi zabin Allah ka kiyaye dokar ubangiji zakayi mamakin matar dazaka samu Amma inde dabiaa Bata chanzaba ubangiji baya diba

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel