Jarumin barkwanci a Kannywood, Gidigo ya yi rashin mahaifi
ALLAH Sarki! Rai baƙon duniya. Allah ya yi wa mahaifin jarumin barkwanci a Kannywood, Alhaji Mika’il Isah Ibn Hassan (Gidigo) rasuwa.
Alhaji Musa Garba ya rasu a ranar Talata, 22 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, a asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke cikin garin Kano, bayan jinya da ya yi na kwana shida.
An yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Laraba a gidan sa da ke unguwa Uku a Jihar Kano.
Dattijon mai kimanin shekaru 82, ya rasu ya bar ‘ya’ya 9, Gidigo ne na farko.
‘Yan Kannywood da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Tahir I. Tahir, Nura Manaja, Abba El-Mustapha, Sadiq Mafia, Aminu Sherif (Momo) da sauran su.
Allah ya jiƙan Baba Musa Garba da rahama.