Matsaloli 6 da rashin shan isasshen ruwa ke haifarwa jikin mutum mace ko namiji - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Matsaloli 6 da rashin shan isasshen ruwa ke haifarwa jikin mutum mace ko namiji

Oct 28, 2024


Matsaloli 6 da rashin shan isasshen ruwa ke haifarwa jikin mutum mace ko namiji


by Naziru Dalha Taura 


Idan aka rasa ruwa, mutum, dabbobi, tsirrai da sauran wasu halittu masu yawa zasu mutu - 


Dukkan halittun jikin mutum na bukatar ruwa domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata - 


Masana sun gano cewa yawan shan ruwa ya fi zama alheri ga jikin mutum a kan karancin shan ruwa Babu jayayya ko tantama a kan muhimmanci da amfanin ruwa a wurin mutane da dabbobi. 


Idan babu ruwa, mutum ba zai rayuwa ba. 


Karancin ruwa kan kassara lafiyar jikin mutum, hakazalika, rashin shan isashen ruwa yana haifarwa da jiki matsaloli.


 Wani binciken kimiyya ya gano cewa masu yawan shan ruwa sun fi koshin lafiya a kan marasa shan isashen ruwa. 


Domin gujewa karancin ruwa a jiki (Dehydration) ana so baligin mutum ya sha ruwa akalla kofi takwas a kowacce rana. 


 Ruwa yana da muhimmanci ga halittun jikin mutum, yana jika makoshi da taimakawa wajen narka abinci a tumbin mutum. 


Matsaloli 6 da rashin shan isashen ruwa ke haifarwa jikin mutum Source: UGC 


Dukkan halittun jikin mutum na bukatar ruwa domin yin aikinsu yadda ya kamata.


 Me zai faru kenan idan mutum ba ya shan isashen ruwa?


 1. Rashin kuzari Idan ruwa ya yi karanci, ko yawansa ya ragu sosai, a jiki, mutum zai ji kasala da rashin kuzari.


 Mutum zai ji ya gaza cigaba da aikinsa. 


2. Hatsarin kamuwa da cutar mutuwar rabin jiki A wani binciki da aka yi a wata cibiyar cututtukan zuciya (BMC Cardiovascular Disorders), an gano cewa karancin ruwa na saka jiki a hatsarin kamuwa da cutuwar mutuwar rabin jiki tare hana warkewa da wuri idan cutar ta samu mutum.


 3. Rashin saurin narkewar abinci a ciki Abincin ba ya saurin narkewa a cikin yayin da mutum ke jin kishin ruwa ko kuma idan babu isashen ruwa a jikinsa.


 4. Ciwon kai Saboda kwakwalwa tana bukatar ruwa, duk lokacin da ya kasance babu wadatarsa a jikin mutum, sai ya ji gajiya da ciwon kai. 


5. Rashin kyan fatar jiki Fatar jikin mutum ta na bukatar ruwa kafin ta kasance cikin yanayi mai kyau.


 A saboda haka, rashin shan isashen ruwa zai sa fatar mutum ta ke bushewa, lamarin da ke saurin tsofar da fata. 


6. Kiba Yawan shan ruwa zai iya taimakawa jiki wajen rage teba. Rashin shan isashen ruwa zai iya sa mutum ya kara kiba.